Khedira zai kasance a Real Madrid har zuwa 2015

Sami Khedira
Image caption Khedira matashin dan kwallo ne da Jamus ke ji dashi

Kungiyar Real Madrid ta ce ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Jamus Sami Khedira na tsawon shekaru biyar daga kungiyar Stuttgart.

Dan shekaru 23 da haihuwa, Khedira ya taka mahimmiyar rawa a tawagar Jamus lokacin gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Manajan Daraktan Stuttgart Fredi Bobic ya ce basu so su barin dan kwallon ya tafi ba, amma dai babu yadda zasu yi saboda shi yanason ya koma Madrid, a don haka suna yi mishi fatan alheri.

Tun komawar Jose Mourinho kungiyar Real Madrid, Khedira ya kasance dan kwallo na biyu da ya koma kungiyar bayan da aka sayi Angel di Maria daga Benfica.

A garan bawul din da Mourinho ya fara yi, tsaffin 'yan wasa Raul da Guti duk sun bar Real Madrid din.