Ba zamu sayar da Cole ba- Ancelotti

Ashley Cole
Image caption Ashley Cole na daga cikin kashin bayan Chelsea

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya kawo karshen maganganu akan Ashley Cole zai koma Real Madrid inda ya jaddada cewar dan wasan na baya ba na sayarwa bane.

Rahotanni sun nuna cewar tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho wanda a yanzu shine mai horadda 'yan wasan Real na bukatar ya sake hadewa dan dan kwallon Ingila.

Ancelotti yace: "Ashley Cole dan wasan Chelsea ne babu inda za shi ko nawa za a bamu".

Mourinho ne ya sayi Cole daga Arsenal a shekara ta 2006 kuma suna dasawa sosai.