Rashin kudi ne yasa Ivory Coast ta sallami Eriksson

Eriksson
Image caption 'Yan kwallon Ivory Coast sun yabawa Eriksson

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast Sory Diabate ya bayyana cewar batun kudi ne ya hana kasar cigaba da rike Sven-Goran Eriksson a matsayin mai horadda 'yan kwallon kasar.

Kasar dai ta tabbatar da cewar Erikson wanda ya jagoranci tawagar Elephants zuwa gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu, ya yi namijin kokari duk da cewar kasar bata tsallake ba zuwa zagaye na gaba.

A cewar Diabate "Mun so mu rike Eriksson, kuma shima yana ya so ya tsaya".

Rahotanni sun nuna cewar Ivory Coast na bukatar makudan kudade idan har tanason ta cigaba da rike Eriksson.

Ivory Coast ta kara ne a rukuni mai sarkakiya tare da Brazil da Portugal da Koriya ta Arewa.