Illimin 'ya'ya mata a jamhuriyar Nijar

Illimin 'ya'ya mata a jamhuriyar Nijar
Image caption Yara mata a Nijar na sha'awar ilimin boko

A jamhuriyar Nijar kimanin yara maza 44 ne bias dari yayin day an mata 31 bisa dari ne ke zuwa makaranta .

A sakamakon haka a lokacin taron duniya akan ilimi da aka gudanar a Dakar babban birnin Senegal a shekara ta 2000 dukkan mahalarta taron daga kasashe 164 daga ciki hadda jamhuriyar Nijar suka lashi takobin cimma wasu manufofi shida game da al'amuran ilimi nan da shekara ta 2015.

Daga cikin wadannan manufofi har da ba da ilimi kyauta ga kowa-da-kowa da kamanta adalci tsakanin maza da mata kuma da illimin yaya mata a kasashe masu tasowa .

Ko da yake a jamhuriyar Nijar rahotani sun nuno cewa akwai ci gaba dangane da yara mata dake zuwa makaranta amma fa ana fama da tafiyar hawainiya a wannan bangare.

A jamhuriyar ta Nijar a yankunan karkara ban an gizo ke saka ba sai dai suna dauke yara ne su masu aure tun kayin suyi shekaru 18 da haihuwa .

Samun yancin kai kawo yanzu ana iya cewa an samu dan cigaba a illimin na yaya mata .

Sannu a hankali komi na sake yanzu yaran ne da kansu keda burin zarcewa da karatun wani lokaci ba tare da son iyayen su ba .

Kungiyoyi da dama da suka hada da Tattali suna kokarin su wajen daukar nauyin yaran 'yan matan ta hanyar sama masu gidajen zama da kuma basu yan kudaden sayen sabini

A sha'anin illimin 'ya'ya mata idan aka duba lokacin samun 'yancin kan nijar kawo yanzu ba karamar nasara aka samu ba gani yanda matan ke bada nasu kokari wajen ci gaban kasar .