FIFA ta ci tarar Spain da Holland

Blatter
Image caption Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA Sepp Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ci tarar zakaran kwallon duniya Spain da kuma abokiyar karawatta a wasan karshen Holland saboda rashin ladabin 'yan wasansu a lokacin wasan.

Fifa ta ci tarar Holland pan dubu tara da tamanin, a yayinda aka ci tarar Spain pan dubu shida da hamsin da uku.

Alkalin wasan wato dan Ingila Howard Webb ya baiwa 'yan kwallon Holland takwas katin gargadi sannan kuma ya kori John Heitinga a wasan da aka tada hankali a Afrika ta Kudu.

Spain ce ta samu nasara a wasan daci daya me ban haushi amma itama an baiwa 'yan wasan biyar katin gargadi.