Torres ya ce ba zai bar Liverpool ba

Torres
Image caption Dan wasan Liverpool Fernando Torres

Dan kwallon Liverpool Fernando Torres ya ce ba zai bar kungiyar ba sannan ya shirya aiki tare da sabon kocinsa Roy Hodgson.

Torres me shekaru 26 anata alakan tashi da Chelsea da Manchester City tun lokacin da kungiyar ta kasa tsallake zuwa gasar zakarun Turai.

Yace"Na shirya taka leda da fuskantar kalubalen dake gabana,kuma ina tare da Liverpool dari bisa dari".

A ranar litinin ne Torres ya koma horo bayan ya taimakawa kasarshi ta lashe gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.