Ghana bata gayyaci Essien da Muntari ba

Black Stars
Image caption Tawagar 'yan kwallon Ghana dai sun taka rawar gani a Afrika ta kudu

Michael Essien da dan kwallon Inter Milan Sulley Muntari na daga cikin manyan 'yan kwallon da Ghana taki gayyata don buga wasan sada zumunci da Afrika ta Kudu a mako mai zuwa.

Kocin Black Stars Milovan Rajevac ya gayyaci wasu 'yan kwallo hadda guda 12 da suka kai zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

A ranar litinin ne, Essien ya buga wasanshi na farko a Chelsea a bana tun bayan daya samu rauni a gwiwarshi.

Haka zalika, babu wata hujjar da aka bayar na kin kiran Muntari da kuma John Pantsil.

Tawagar Ghana:

Masu tsaron gida: Richard Kingson (unattached), Daniel Agyei (Liberty Professionals).

Masu buga baya: Samuel Inkoom (Basel, Switzerland), Harrison Afful (Esperance, Tunisia), John Mensah (Lyon, France), Lee Addy (Bechem Chelsea), Jonathan Mensah (Granada, Spain).

Masu buga tsakiya: Anthony Annan (Rosenborg, Norway), Emmanuel Agyemang-Badu (Udinese, Italy), Kwadwo Asamoah (Udinese, Italy), Andre Ayew (Marseille, France), Kevin-Prince Boateng (Portsmouth, England), Cofie Bekoe (Petrojet, Egypt), Bernard Kumordz (Panionios FC, Greece).

Masu buga gaba: Asamoah Gyan (Rennes, France), Dominic Adiyiah (AC Milan, Italy), Haminu Draman(Lokomotiv Moscow, Russia), Yaw Antwi (FK Vojvodina, Serbia).