Fabregas ya koma horo a filin Emirates

Fabregas
Image caption Arsenal Captain Cesc Fabregas

Cesc Fabregas ya koma horo tare da sauran 'yan kwallon Arsenal a ranar alhamis abinda kuma ke nuna cewar yananan daram a matsayin kaptin din kungiyar.

Fabregas ya nuna aniyarshi na komawa tsohuwar kungiyarshi Barcelona a karshen kakar data wuce, amma dai har yanzu ba a warware takaddama ba akanshi saboda Arsenal din tana son Barca ta biya pan miliyan 30.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya nuna cewar baya son ya saki Fabregas akan ko nawa ne, amma dai manyan 'yan kwallon Barca din sun fito fili cewar sun zaku angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Magoya baya Arsenal akalla 10,000 ne suka tarbi Fabregas a filin Emirates lokacin daya shigo horon.