Har yanzu Aaron Makoena ne kaptin din Bafana Bafana

Makoena
Image caption Kaptin din Bafana Bafana Aaron Makoena

Sabon kocin Afrika ta Kudu Pitso Mosimane ya ce ba ba zai canza Aaron Mokoena a matsayin kaptin din Bafana Bafana.

Abinda hakan ke nufi shine Makoena ne zai jagoranci sauran 'yan kwallon a wasan sada zumunci tsakanin Bafana Bafana da Black Stars na Ghana a mako mai zuwa a filin wasa na Soccer City.

An dai zargi Mokoena cewar sakacinshi ne yasa a zira wasu kwallaye a ragar Afrika ta Kudu a gasar cin kofin duniya, abinda kuma ya hanata tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Sabon kocin Bafana Bafana din Mosimane wanda ya maye gurbin Carlos Alberto Parreira a watan daya wuce, ya cigaba da 'yan wasa 17 cikin 23 da suka buga gasar cin kofin duniya.

'Yan kwallon da aka gayyata:

Masu tsaron gida: Moeneeb Josephs (Orlando Pirates), Itumeleng Khune (Kaizer Chiefs)

Masu buga baya: Bevan Fransman (Hapoel Tel Aviv, Israel), Siboniso Gaxa (Mamelodi Sundowns), Morgan Gould (SuperSport Utd), Tsepo Masilela (Maccabi Haifa, Israel), Innocent Mdledle (Orlando Pirates), Aaron Mokoena (Portsmouth, England), Anele Ngcongca (Racing Genk, Belgium), Siyabonga Sangweni (Golden Arrows)

Masu buga tsakiya: Daine Klate and Teko Modise (both Orlando Pirates), Reneilwe Letsholonyane and Siphiwe Tshabalala (both Kaizer Chiefs), Kagisho Dikgacoi (Fulham, England), Thanduyise Khuboni (Golden Arrows), Surprise Moriri (Mamelodi Sundowns), Macbeth Sibaya (Rubin Kazan, Russia), Steven Pienaar (Everton, England

Masu buga gaba: Katlego Mphela (Mamelodi Sundowns), Sthembiso Ngcobo (KaizerChiefs), Bernard Parker (Twente, The Netherlands)