Lagerback ya yi watsi da Najeriya

Tsohon kocin Najeriya Lars Lagerback
Image caption Jama'a da dama sun soki hanyoyin da aka nada Lars Lagerback

Kociyan da ya kai tawagar Super Eagles ta Najeriya zuwa gasar cin kofin duniya Lars Lagerback ya yi watsi da bukatar ci gaba da jagorantar kungiyar.

A wata wasika ta ya aikawa Hukumar Kula da Kwallon kafa ta Najeriya NFF, Lagerback ya ce ba zai ci gaba da jagorantar Super Eagles ba.

Shi ne dai ya jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Afrika ta Kudu, inda aka fitar da kasar a zagayen farko.

Wasu rahotanni a kafafen yada labarai na kasar sun nuna cewa hukumar ta NFF ta baiwa kociyan dan shekaru 62 damar ci gaba da aikin nasa.

Amma Dominic Iorfa, wanda shi ne shugaban kwamitin kwararru na hukumar, ya shaidawa BBC cewa Lagerback ya yi watsi da tayin.

"Ya ce tayin na da kyau sosai, amma ba shi da sha'awar ci gaba," a cewar Lorfa

Wasu magoya bayan kasar da kuma kafafen yada labarai na cikin gida za su yi maraba da matakin da kociyan ya dauka.

A yanzu ana hasashen tsohon dan wasan kasar, kuma tsohon kociyan tawagar 'yan kasa da shekaru 20, Samson Siasia ne zai zamo kociyan tawagar ta Super Eagles.

Amma Lorfa ya dage cewa NFF za ta yi tunani sosai kafin ta sanar da sabon kociyan kasar.

Siasia ka iya fuskantar kalubale daga takwarorinsa irinsu Stephen Keshi da Sunday Oliseh da Austin Eguavoen da Emmanuel Amuneke wajen neman wannan aiki.

Najeriya za ta fara buga wasan ta na neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da kasar Madagascar a ranar 4 ga watan Satumba.