Tottenham za ta kara da Young Boys

'Yan wasan kungiyar Tottenham
Image caption 'Yan wasan kungiyar Tottenham

Kungiyar Tottenham ta Ingila za ta kara da kungiyar Young Boys ta kasar Switzerland a wasanni share fage a gasar zakarun Turai.

Kungiyar Spurs dai ta kubuta ne daga haduwa da kungiyoyi kamarsu Dynamo Kiev da Sampdoria da kuma Auxerre.

Tottenham za ta buga wasan farko ne a Berne a ranar 17 da 18 ga watan Agusta sanan kuma ita kuma Young Boys za ta garzaya White Hart Lane a ranar 24 da 25 ga watan Agusta.

Kugiyar Yung Boys bata taba taka leda ba a gasar zakarun Turai.