Manchester City na gabda sayen Milner da Balotelli

Milner da Balotelli
Image caption James Milner da Mario Balotelli

Manchester City ta ce tana saran za ta kamalla kulla yarjejeniya da dan kwallon Aston Villa James Milner dana Inter Milan Mario Balotelli daga nan zuwa ranar Alhamis.

A makon daya gabata ne Kocin Villa Martin O'Neill yace Milner zai koma Manchester City.

Villa dai taki amince da tayin pan miliyan 20 aka Milner daga City inda tace sai an biya pan miliyan 30.

Kocin City Roberto Mancini yace"Muna gabda kulla yarjejeniya da 'yan kwallon biyu"

Idan har aka kulla yarjejeniyar biyu, tabbas City ta kashe fiye da pan milyan 125 abinda kuma ke tabbatar da cewar itace kungiyar data fi kowacce kudi a duniya.