Paul Robinson ya yi ritaya a Ingila

Robinson
Image caption Paul Robinson a lokacin da Ronaldinho ya ci Ingila a 2006

Golan Blackburn Rovers Paul Robinson ya ce yayi ritaya daga bugawa kwallo.

Robinson wanda aka saka cikin tawagar 'yan kwallon Ingila wandanda zasu buga wasan sada zumunci da Hungary a ranar laraba mai zuwa, ya ce ba zai buga ba.

Dan shekaru 30 da haihuwa, Robinson ya buga gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006 kafin a daina jin duriyarshi a Ingila.

Tsohon golan Leeds da Tottenham, Robinson ya zama golan Ingila a karon farko a shekara ta 2003 kuma ya kama mata gola sau 41 hadda wasanni biyar daya kama a gasar cin kofin duniya a Jamus a shekara ta 2006.