Manchester United ta daga kofin Community Shield

Ferguson
Image caption Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson

Manchester United ta samu galaba akan Chelsea a wasan kofin Charity Shield wanda aka yi dauki ba dadi sosai tsakanin kungiyoyin biyu a filin wasa na Wembley.

Antonio Valencia ne ya ciwa Manchester United kwallon farko bayan da Wayne Rooney ya bashi kwallon sannan daga bisani Javier Hernandez ya ci biyu.

Salomon Kalou ne ya farkewa Chelsea kwallo daya a yayinda Dimitar Berbatov ya ciwa United na uku inda aka tashi United nada ci uku Chelsea nada ci daya.

A lokacin wasan dai an yiwa wadanda suka bugawa Ingila kwallo ihu.