Wes Brown ya yi ritaya daga bugawa Ingila kwallo

Brown
Image caption Dan kwallon Manchester United Wes Brown

Dan kwallo na bayan Manchester United Wes Brown ya sanarda yin ritaya daga bugawa Ingila kwallo.

Dan shekaru 30 da haihuwa sanarwar ta Brown ta zo jim kadan bayan da golan Balckburn Paul Robinson yayi ritaya.

Duka 'yan kwallon biyu na cikin tawagar da Ingila ta gayyata don buga wasan sada zumunci tsakaninta da Hungary a ranar Laraba.

Hukumar kwallon Ingila wato FA ta tabbatar da cewar Brown ya ziyarci otal din 'yan Ingila a Watford a ranar Lahadi don ya bayyanawa Fabio Capello hukuncin daya yanke.

Brown yace" A shekara 30, ina ganin cewar wannan ne lokacin da ya kamata in matsa in baiwa matasa dama, don ni kuma in maida hankali a kungiyata".