Capello ya nemi afuwar magoya bayan Ingila

Capello
Image caption Kocin Ingila Fabio Capello

Kocin Ingila Fabio Capello ya nemi afuwar magoya bayan Ingila wadanda suka tafi Afrika ta Kudu don kallon gasar cin kofin duniya, inda kasar bata taka rawar gani ba.

Capello mai shekaru 64 ya sha kakkausar suka bayan da Jamus ta lallasa Ingila daci hudu da daya a wasan zagaye na biyu. Sannan kuma Ingilar ta sha da kyar a karawarta da Amurka da Algeria da Slovenia a wasan rukuni.

Da yake jawabi ga manema labarai, Capello ya nemi magoya bayan su yafe mashi sannan kuma ya ce baisan dalilan da suka sanya 'yan wasanshi suka kasa taka rawar gani ba.

Capello yace"da farko, ina neman afuwar magoya saboda rashin haskakawarmu a gasar cin kofin duniya".

Ya kara da cewar"mun sani magoya bayan sun kashe makudan kudade can a Afrika ta Kudu".