Inter:Maicon ba zai koma Real Madrid ba

Maicon
Image caption Dan Brazil mai taka leda a Inter Milan Maicon

Shugaban kungiyar Inter Milan Massimo Moratti ya ce dan wasanshi na baya Maicon ba zai koma Real Madrid ba.

Moratti ya kawo karshen cece-kuce akan cewar Maicon zai hade da tsohon kocinsa wato Jose Mourinho.

Kungiyoyin biyu wato Inter da Real dai sun kasa cimma matsaya akan darajar dan kwallon, abinda kuma ya sanya Moratti ya bayyana cewar Maicon ba zai tafi ba.

Moratti yace"Maicon ba zai bar Inter ba, wasu kungiyoyi na zawarcinshi amma ba zamu sayar dashi ba".

Rahotanni sun nuna cewar Real ta nemi a bata dan kwallon akan Euro miliyan 24 a yayinda ita kuma Inter ke neman Euro miliyan 30 akanshi.