Zan iya yiwa Ingila ihu- In ji Gerrard

Steven Gerrard
Image caption Steven Gerrard

Kyaftin din tawagar Ingila Steven Gerrard ya ce da shi dan dan kallo ne zai yiwa 'yan wasan Ingila ihu a wasan da kasar za ta buga da Hungary ranar laraba.

Kyaftin din Ingila ya ce yana kyautata zaton 'yan kallo za su yi musu ihu, saboda mumunar rawar da suka taka a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu.

Manema labarai sun tabayi Gerrard ko zai iya yiwa 'yan wasan kasar ihu, da ace shi dan kallo ne, sai ya ce; "Kwarai da gaske zanyiwa tawagar kasar ihu".

Ya kara da cewa: "Dolene munyi hakuri da hakan domin magoya bayan mu sun fusata saboda mun basu kunya".

Ingila ta sha kashi ne a wasan da ta buga da Jamus a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu da ci hudu da guda.

Kasar dai ta lashe wasa guda ne cikin hudu da ta buga a gasar.