FIFA na binciken gallazawa 'yan kwallon Koriya ta Arewa

Zuma da Blatter
Image caption Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma da Sepp Blatter na FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fara gudanar da bincike akan rahoton cewar an gallazawa 'yan kwallon Koriya ta Arewa bayan sun kasa taka rawar gani a gasar cin kofin duniya.

Bayan da 'yan kwallon Koriya ta Arewa suka yi gurmuzu tsakaninsu da Brazil a Afrika ta Kudu, sai gwamnatin kasar ta bada umurnin a saka wasansu da Portugal kai tsaye a gudajen talabiji amma sai Portugal din ta casa su daci bakwai da nema.

Wani gidan rediya ya bayyana cewar sakamakon haka sai aka ladabtarda 'yan kwallon sannan kuma aka saka kocinsu aikin karfi.

Shugaban FIFA Sepp Blatter ya ce an fara binciken lamarin.