Ivory Coast ta raba gari da Gerrard Gili

Drogba
Image caption Drogba nashe nashe akan ciyawa

Dan Faransa Gerard Gili ya ce baida bukatar zama sabon mai horadda 'yan kwallon kasar Ivory Coast.

Tattaunawa tsakanin Gili da hukumar kwallon kasar Ivory Coast ya kawo karshe ne bayanda Gili ya taho tare da mataimakanshi a yayinda su ita kuma hukumar kwallon Ivory Coast tace sai dai ya dauka daga cikin wasu kocinta na cikin kasar.

Kocin riko Francois Zahoui wanda ya jagoranci Ivory Coast ta doke Italiya daci daya da nema ya ce baya tunanin rike mukamin na dun dun dun.

Kolo Toure ne ya zira kwallo da kai bayan a dawo hutun rabin lokaci.