John Mensah ya koma Sunderland

Mensah
Image caption Dan kwallon Ghana John Mensah

Sunderland ta kamalla kulla yarjejeniya na sayen dan kwallon Ghana John Mensah daga kungiyar Lyon.

Dan shekaru 27 da haihuwa, Mensah zai kasance tare da Sunderland na wucin gadi a kakar wasan da za a shiga.

Kocin Sunderland Bruce ya shaidawa BBC cewar "dan kwallo ne me kyau, kuma duk wanda yaga yadda yayi kwallo a bara zai san cewar ba abin yarwa bane".

Mensah shine a sanya kambum kaptin din Ghana a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu inda Black Stars din suka kai zagayen gabda na kusada karshe.