Real Madrid ta sayi Carvalho daga Chelsea

Carvalho
Image caption Dan kwallon Portugal Ricardo Carvalho

Real Madrid na gabda kamalla kulla yarjejeniya da dan kwallon Portugal Ricardo Carvalho wanda ke taka leda a Chelsea.

Real ta amince akan bada pan miliyan 6.7 don Carvalho ya hade da tsohon kocinsa na a Chelsea Jose Mourinho.

Sanarwa daga yanar gizon Chelsea ta ce"mun amince tsakaninmu da Real Madrid don Carvalho ya koma taka mata leda"

Carvalho, a baya yana tare da Mourinho a FC Porto kafin ya koma Chelsea a shekara ta 2004 akan pan miliyan 19.8.

A shekaru biyar din da Carvalho ya shafe a Chelsea, ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar premier sau uku da kuma kofin FA sau uku da kuma Community Shield sau biyu.

Carvalho ya kasance dan kwallo na biyar da Real ta siya a kwanannan, bayan ciki hadda Angel di Maria da Pedro Leon da Sergio Canales da kuma Sami Khedira.