Lerner:Abinda yasa O'Neill ya bar Aston Villa

ONeill
Image caption Kocin Aston Villa Martin O'Neill

Mai Aston Villa Randy Lerner ya ce Martin O'Neill ya bar mukaminshi ne saboda su biyun nada bambamcin ra'ayi akan yadda za a ciyar da kungiyar gaba.

O'Neill a ranar litinin ne ya yi murabus bayan shafe shekaru hudu a matsayin, a yayinda aka baiwa Kevin MacDonald a matsayin kocin riko.

Lerner ya kara da cewar "Abinda zamu maida hankali akai shine mu baiwa Kevin MacDonald goyon bayan sannan kuma mu kawo karshen batun komawar James Milner zuwa Manchester City."

A halin yanzu dai kocin Amurka Bob Bradley dana kungiyar Ajax Martin Jol da tsohon dan kwallon Jamus Jurgen Klinsmann da kuma Sven-Goran Eriksson na daga cikin wadanda ke son a basu mukamin.