Chelsea ta kammala siyan Ramires

Ramires
Image caption Ramires ya taka leda a gasar cin kofin duniya

Chelsea ta sayi dan wasan Brazil Ramires a kudi fam miliyan 17 daga kungiyar Benfica.

"Dan wasan kwararre ne ," In ji kocin Chelsea Carlo Ancelotti. "Zai taka rawar gani a tawagar Brazil nan gaba, ina kuma fatan zai sake nuna hakan a Chelsea."

Ramires mai shekarun haihuwa 23 ya koma kungiyar Benfica ne daga kungiyar Cruzeiro a bara a kan kudi fam miliyan shida.

Dan wasan ya takawa Brazil leda sau goma sha bakwai.

Ramires shine dan wasa na biyu da Chelse ta siya bayan zuwan Yossi Benayoun daga kungiyar Liverpool.