Wenger sai ci gaba da horon Arsenal

Arsene Wenger
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya bayana cewar yana dab da sa hannu a kwantaragin da zai sa ya ci gaba da jagorantar kungiyar.

Kwantaragin Kocin mai shekarun haihuwa 60 sai kare ne a karshen kakkar wasan bana, amma ya ce ya kusa ya sa hannu a kwantaragi domin ci gaba da horon kungiyar.

"Ya kamata in nuna cewa ina da kwarin gwiwa game da kungiyar". In ji Wenger.

Wenger ya lashe kofina 11 a shekaru 13 da ya yi a Arsenal, amma dai kungiyar ta gagara lashe wani kofin tun bayan gasar FA da ta lashe a shekarar 2005.

Arsenal za ta fara buga wasanta na farko ne da kungiyar Liverpool a gasar Premier ta kakkar wasanni bana a ranar Lahadi.