Sevilla ta kunyata Barcellona a Spain

Barca
Image caption Motar daukan 'yan kwallon Barca

Sevilla tayi bazatan farkewa kwallon farkon da Barcelona ta zira mata, inda tayi kukan kura ta lallasa Barca din daci uku da daya a bugun farko na cin kofin Super na Spain.

Dan Sweden Zlatan Ibrahimovic ne ya bude fagen minti 20 da fara bayan Maxwell ya bashi pasin.

Amma da aka dawo hutun rabin lokaci sai dan Brazil Luis Fabiano ya farkewa Sevilla sannan kuma sai dan Mali Freddie Kanoute yaci kwallaye biyu inda aka tashi uku da daya.

A ranar Asabar 21 ga watan Agusta za ayi bugu na biyu.