Liverpool ta tashi kunen doki tsakaninta da Arsenal

Ngog
Image caption David Ngog ne ya ciwa Liverpool kwallo

Kuskure daga wajen golan Liverpool Pepe Reina ne janyo Arsenal ta farke kwallo daya inda aka tashi kunen doki tsakanin kungiyoyin biyu a wasan premier.

A lokacin wasan dai an baiwa Joe Cole jan kati saboda tokarin daya kaiwa Laurent Koscielny kafin David Ngog ya ciwa Liverpool kwallon farko.

Arsenal ta yi takai hare hare amma ta kasa ci har sai da Marounae Chamakh ya buga kwallo ta taba karfen ragar Liverpool sai golan Liverpool din Reina ya ci kanshi.

Wannan ne wasan farko da Roy Hodgon ya jagoranci Liverpool a wasan premier.