Dan Ingila ne zai gaji Fabio Capello

Capello da Beckham
Image caption Kocin Ingila Fabio Capello da David Beckham a Afrika ta Kudu

Hukumar kwallon Ingila wato FA ta ce dan Ingila ne zai maye gurbin Fabio Capello a matsayin mai horadda 'yan kwallon kasar.

Capello wanda dan Italiya ne sai a shekara ta 2012 ne kwangilarshi za ta kare da Ingila, amma dai yana fuskantar matsin lamba saboda Ingila tayi abun kunya a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Manajan Darektan FA Andrian Bevington yace"Ina tunanin cewar wanda zai maye gurbin Capello a nan gaba zai zama dan asalin Ingila ne".

Ana zargin tsohon kocin AC Milan da Real Madrid din cewar babu fahimta a tsakaninshi da 'yan kwallon Ingila saboda bambamcin harshe, sannan kuma bai saka fikra ba wajen yadda ya bayyanawa David Beckham yayi ritaya.