Real Madrid ta doke Bayern Munich

Ronaldo
Image caption Christiano Ronaldo yana farin jini a Bernabeu

Real Madrid ta doke Bayern Munich a bugun penariti daci hudu da biyu inda ta daga kofin Franz Beckenbauer a filin wasa na Allianz Arena.

Iker Casilas shine yafi haskakawa a wasan inda ya kabe bugun penariti uku daya ana cikin wasa, biyu kuma bayan an tashi ana neman kungiyar da zata zama zakara.

An dai shafe minti 90 ana gurmuzu tsakanin 'yan Real Madrid karkashin jagorancin Jose Mourinho da kuma 'yan Bayern karkashin jagorancin Loius van Gaal, amma dai babu ci.

A bugun penaritin dai Ronaldo daVan der Vaart da Xabi Alonso da Karim Benzema duk sun ciwa Real kwallo a yayinda Altintop da Braafheid suka bararwa Bayern Munich.