Bayan shekaru 25, Najeriya za ta cika wa Golden Eaglets alkawari

Nduka
Image caption Nduka Ugbade ne ya rataya kambum kaptin din Golden Eaglets a 1985

Gwamnatin Najeriya ta ce zata cika alkawarin data yiwa tawagar 'yan kwallon golden eaglets wadanda suka lashe gasar cin kofin duniya ta 'yan kasada shekaru 16, shekaru 25 da suka wuce.

A wancan lokaci dai an yiwa kowanne dan kwallo alkawarin gida, da hannu jari a babban banki kasar da kuma daukar dawainiyar karantansa saboda takawa rawar ganin da suka yi a shekarar 1985.

Amma dai sai suka ji shuru kamar an shuka dusa.

Kaptin din tawagar Nduka Ugbade ne ya kai koken kin cika alkawarin gaban majalisar wakilan Najeriya, inda ya kece da hawaye saboda takaici.

Darektan Janar na hukumar wasannin kasar Patrick Ekeji ya nemi afuwar 'yan kwallon kuma ya yi alkawarin zai bi kadin zancen.