An dakatar da Joe Cole na wasanni uku

Joe Cole
Image caption Dan kwallon Liverpool Joe Cole

An dakatar da dan kwallon Liverpool Joe Cole na wasanni uku sakamakon jan katin da aka bashi a wasansu da Arsenal.

Alkalin wasa Martin Atkinson ne ya baiwa Cole jan kati bayan ya tokari Laurent Koscielny inda aka tashi wasan daya da daya.

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya ce bazasu daukaka hukuncin ba.

Cole dai ya bar Chelsea a kwannan nan, kuma ba zai buga wasannin Liverpool da Manchester City da West Brom da Birmingham.

Amma dai zai buga wasan Europa a ranar Alhamis tsakanin Liverpool da Trabzonspor.