An kebe 'yan kwallo 12 da za a basu kyauta a Turai

Uefa
Image caption Tambarin UEFA

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney ne kadai dan Ingila cikin 'yan kwallon 12 da hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA ta kebe don bada kyautar gwarzon dan kwallon klub din Turai.

Sauran wadanda ke takarar kyautar sune Lionel Messi na Barcelona da Diego Milito na Inter Milan.

Cikakken wadanda ake kebe:

Golan Uefa na bana:

Júlio César (Internazionale)

Hugo Lloris (Olympique Lyonnais)

Víctor Valdés (Barcelona)

Dan wasan baya na bana:

Lúcio (Internazionale)

Maicon (Internazionale)

Gerard Piqué (Barcelona)

Dan wasan tsakiya na bana:

Xavi Hernández (Barcelona)

Arjen Robben (Bayern Munich)

Wesley Sneijder (Internazionale)

Dan wasan gaba na bana:

Lionel Messi (Barcelona)

Diego Milito (Internazionale)

Wayne Rooney (Manchester United)

Masu horadda 'yan kwallon na kungiyoyi 16 da suka kai zagayen gabda na kusada karshe ne ke zaban wadanda za a baiwa kyautar.

Kuma a ranar 26 ga watan Agusta ne za baida kyautukan a lokacin bukin rarraba kungiyoyi na gasar zakarun Turai na bana a birnin Monaco.