Faransa ta dakatar da Nicolas Anelka

Anelka
Image caption Nicolas Anelka a lokacin da aka kori daga Afrika ta Kudu

Hukumar kwallon kasar Faransa ta dakatar da Nicolas Anelka na tsawon wasanni 18 saboda yanayin yadda ya gudanar da kanshi a gasar cin kofin duniya.

Kocin Faransa Raymond Domenech dai ya kori Anelka daga Afrika ta Kudu bayanda tawagar 'yan kwallon Faransa suka yi zanga zanga kuma suka ki fitowa horo.

Patrice Evra wanda shine Kaptin din tawagar an dakatar dashi na wasanni biyar saboda nashi laifin.

Shi kuwa Franck Ribery an dakatar dashi ne na wasanni uku a yayinda aka dakatar da Jeremy Toulalan daga buga wasa guda.