Manchester City ta sayi Milner akan pan miliyan 26

Milner
Image caption James Milner ne dan kwallo na shida na City ta saya da tsada

Dan kwallon Ingila James Milner ya kamalla kulla yarjejeniya da Manchester City akan pan miliyan 26 daga kungiyar Aston Villa.

A bisa tsarin yarjejeniyar kuma, sai da City din ta bada dan kwallonta Stephen Ireland ya koma Aston Villa.

An shafe makwanni anata tattaunawa tsakanin Aston Villa da Manchester City akan Milner din kafin a sasanta a ranar Laraba.

Batun sayarda Milner dai shine ya janyo takaddama har Martin O Neill ya bar Aston Villa a matsayin mai horadda 'yan kwallon.