Dan kwallon Arsenal Sami Nasri yaji rauni

Nasri
Image caption Arsenal Player Sami Nasri

Dan kwallon Arsenal na tsakiya Samir Nasri ba zai taka leda na wata guda ba saboda ciwon gwiwa.

Dan shekaru 23 da haihuwa, Nasri ya shafe lokaci mai tsawo yana jinyar kararriyar kafarshi a bara, sannan kuma a yanzu ya turgude lokacin wasan Arsenal da Liverpool wanda aka tashi daya da daya.

Wannan raunin ba zai yiwa Arsenal dadi ba ganin cewar Cesc Fabregas baida lafiya, Alex Son yana fama da rauni, Denilson da Aaron Ramsey duk suma ba lafiyar ta ishesu ba.

Nasri dai bai bugawa Faransa gasar cin kofin duniya ba a Afrika ta Kudu amma dai ya buga mata wasan sada zumunci tsakaninta Norway.