Real Madrid ta sayi Mesut Ozil daga Werder Bremen

Ozil
Image caption Mesut Ozil ne ya zira kwallo a ragar Ghana a gasar cin kofin duniya

Real Madrid ta kamalla kulla yarjejeniya da dan kwallon Jamus Mesut Ozil daga kungiyar Werder Bremen.

Dan shekaru 21 da haihuwa, Ozil ya haskaka matuka a tawagar Jamus a gasar cin kofin duniya abinda kuma ya sanya manyan kungiyoyin Turai keta rububi akanshi.

Kungiyoyin biyu sun amince akan Euro miliyan 15 a kwangilar dan kwallon wanda ya kamata ya bar Bremen a badi.

A ranar laraba Ozil za a gwada lafiyarshi a Real din.

Ozil yabi sawun takwaranshi na Jamus Samu Khedira zuwa Bernabeu, kuma ana ganin zai taka mahimmiyar rawa a kungiyar.

Ozil ya kasance daya daga cikin sabbin 'yan kwallon da sabon kocin Real Jose Mourinho ya saya bayan zuwan Khedira da Ricardo Carvalho, da Pedro Leon da Sergio Canales da kuma dan Argentina Angel di Maria.