Dan kwallon Gabon Daniel Cousin ya bar Hull City

Cousin
Image caption Kaptin din Gabon Daniel Cousin

Kaptin din Gabon Daniel Cousin ya bar kungiyar Hull City ta Ingila zuwa kugiyar Larissa ta Girka.

Cousin mai shekaru 33 da haihuwa ya kulla yarjejeniya ta shekaru biyu da kungiyar bayanda a bara yaje mata a matsayin dan kwallon aro.

Dan kwallon ya koma Hull ne a shekara ta 2008 daga Rangers inda ya ci kwallaye biyar a wasanni 33 daya buga mata.

Ficewarshi daga Hull City na daga cikin garan bawul din da kungiyar keyi bayan ta bar gasar Premier zuwa Championship.