AC Milan ta sayi Kevin-Prince Boateng

Kevin-Prince Boateng
Image caption Kevin-Prince Boateng

AC Milan ta sayi dan wasan Ghana Kevin-Prince Boateng na wucin gadi daga kungiyar Genoa. Dan wasan ya koma kungiyar Genoa ne daga Portsmouth, sannan kuma kungiyar ta bada aronshi ga AC Milan. Genoa ta sayi dan wasan ne mai shekaru haihuwa 23, fam miliyan 6.5, kuma tana neman riba ne akan dan wasan shiya sa ta bada shi aro ga AC Milan.

"Ban damu game da yadda na zo kungiyar Inter Milan ba, amma zan nuna kishi da kuma goyon baya ga kungiyar dari bisa dari." inji Boateng.