Cole ya nemi gafara kan fenaritin da ya barar

Joe Cole
Image caption Joe Cole

Dan wasan Liverpool Joe Cole ya ce shine ke da laifi bayan kungiyar ta tashi 1-0 a wasan ta Trabzonspor a wasannin share fage na gasar Europa.

Cole ya barar da fenaritin da aka baiwa kungiyar ne, bayan Ryan Babel ya zura kwallon guda a wasan.

"Gaskiya banji dadin lamarin ba," . "Ban buga fenaritin da kyau ba". inji Cole

Ya kara da cewa; "Ban buga fenariti na kusan tsawon shekaru 15, kuma ina ganin bazan samu damar buga wani ba har na tsawon wasu shekaru 15 kuma."

An dai nunawa Cole jan kati a wasan shi na farko daya bugawa Liverpool a gasar Premier da Arsenal.