Ferdinand zai dawo cikin makwanni biyar

Rio Ferdinand
Image caption Rio Ferdinand

Ana sa ran dan wasan bayan Manchester United Rio Ferdinand zai dawo taka leda a karshen watan Satumba inji kocin kungiyar Sir Alex Ferguson.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 31 ya samu rauni ne ana dab da fara gasar cin kofin duniya da aka kamala a kasar Afrika ta kudu.

Dan wasan dai ba zai samu damar taka leda ba a wasan da kungiyarshi za ta buga da Fulham da West Ham da Everton da kuma Liverpool, amma ana san ran zai buga wasa da Bolton a ranar 26 ga watan Satumba.

Har wa yau dai ba zai samu damar bugawa Ingila wasanni share fage na gasar cin kofin Turai da kasar za ta buga da Bulgaria da kuma Switzerland.