Newcastle na gabda sayen dan Ivory Coast Cheick Tiote

Cheick Tiote
Image caption Dan kwallon Ivory Coast Cheick Tiote

Newcastle na gabda kulla yarjejeniya da dan kwallon Ivory Coast Cheick Tiote wanda ke taka leda a kungiyar FC Twente ta Holland.

Dan shekaru 24 an gwada lafiyarshi kuma yana jiran takardun izinin shiga kasar ne kawai.

Kocin Newcastle Chris Hughton yace"Zai taimaka mana sosai a tsakiya, dan kwallon ne me kyau".

Tiote na daga cikin 'yan kwallon FC Twente da suka lashe gasar kasar Holland kuma ya buga duka wasanni Ivory Coast uku a gasar cin kofin duniya.

Akwai alamun cewar Cheick Tiote zai buga wasan Newcastle da Wolves a ranar Asabar mai zuwa.