Fulham ta jikawa Manchester United gari

Fulham
Image caption 'Yan kwallon Fulham na murnar tashi biyu da biyu tsakaninsu da Man United

Dan kwallon Fulham Brede Hangeland ya ci kwallaye biyu daya a ragarsu daya kuma a ragar Manchester United inda aka tashi biyu da biyu tsakanin kungiyoyin biyu a gasar premier ta karshen mako.

Paul Scholes ne ya fara bude fage inda yaci wa United kwallon farko kafin Simon Davies ya farkewa Fulham.

Dan kwallon United Nani ya samu damar baiwa kungiyarshi nasara a wasan, amma sai golan Fulham David Stockdale ya kabe penaritin daya buga.

Sakamakon wasan ba zai yiwa United dadi ba ganin cewar Arsenal da Chelsea duk sun samu nasara a nasu wasannin.