William Gallas ya koma Tottenham

Gallas
Image caption Dan kwallon Faransa Gallas

Tottenham ta kamalla kulla yarjejeniya da tsohon dan kwallon Arsenal da Chelsea William Gallas.

Ba Faranshen mai shekaru 33, zai kasance tare da Spurs har na tsawon shekara guda.

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce "dan kwallon bai tambayi makudan kudade ba, kuma kudinshi na mako mako baida yawa".

An fahimci cewar Gallas ya amince a biyashi kudi mara yawa a Spurs bayan yaki amince da a rage yawan kudin da ake bashi a Arsenal abinda kuma ya sanya ya fice daga kungiyar.