Messi ya taimakawa Barca ta daga kofin Super

Messi
Image caption Lionel Messi ya ci kwallaye uku shi kadai a ragar Sevilla

Dan kwallon Barcelona Lionel Messi ya zira kwallaye uku a wasan da Barca din ta lashe kofin Super na Spain,bayan ta lallasa Sevilla a ranar lahadi daci hudu da nema.

Wannan nasarar ta nuna cewar Barca din ta casa Sevilla daci 5 da 3 bayan bugu biyu tsakanin kungiyoyin biyu.

'Yan kwallon Barca dai sun nunawa na Sevilla cewar ruwa ba tsaran kwando bane inda Abdoulay Konko yaci kansu minti 13 da fara wasan.

Sannan sai Messi yaci kwallo a minti na 24 da 43 da 90.

Dan kwallon Argentina Messi dai shine yaci kasuwa sosai inda ya lullube sabon dan kwallon Barca wanda aka siyo daga Valencia wato David Villa a yayinda 'yan kwallo 67,000 suka cika filin Nou Camp.