Newcastle ta casa Aston Villa daci shida

Andy Carroll
Image caption Dan kwallon Newcastle Andy Carroll

Andy Carroll yaci kwallaye uku a yayinda Kevin Nolan yaci biyu a wasan Newcastle ta lallasa Aston Villa daci shida da nema.

Joey Barton ne ya fara ciwa Newcastle kwallo sannan sai Nolan yaci kwallo da kai kafin Carroll yaci kwallo daya dabda hutun rabin lokaci.

Carroll yaci kwallonshi na biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci sannan sai Nolan yaci na biyar a yayinda Carroll yaci kwallonshi na uku.

John Carew ne ya barnatar damar Aston Villa tunda farko a lokaci ana babu inda ya barar da bugun penariti.

Sakamakon wasu wasanni premier na mako na biyu:

* Arsenal 6-0 Blackpool * Birmingham 2-1 Blackburn * Everton 1-1 Wolves * Stoke 1-2 Tottenham * West Brom 1-0 Sunderland * West Ham 1-3 Bolton * Wigan 0-6 Chelsea