Roger Federer ya lashe gasar Cincinnati Masters

Federer
Image caption Roger Federer ne ya lashe Cincinnati Masters a 2005, 2007 da 2009

Roger Federer ya doke Mardy Fish da seti uku da biyu a wasan karshe na gasar Cincinnati Masters, abinda ya zama kofin farko daya lashe tun watan Junairun bana a Australian Open.

Federer wanda dan kasar Switzerland ne ya yarfe zusa sosai a kokarinshi na doke Fish dan Amurka.

Wannan nasarar kuma za ta baiwa Federer kwarin gwiwa a yayinda za a fara gasar US open a ranar 30 ga watan Agusta.

A halin yanzu kuma Roger Federer ya kamo Bjorn Borg a matsayin wanda ya lashe gasar Cincinnati Masters har sau biyar.