Brescia ta sayi dan kwallon West Ham Diamanti

Alessandro Diamanti
Image caption Sabon dan kwallon Brescia Alessandro Diamanti

Kungiyar West Ham ta Ingila ta sayarwa kungiyar Brescia ta Italiya dan kwallonta Alessandro Diamanti akan Euro miliyan biyu da dubu dari biyu. akan Euro miliyan biyu da dubu dari biyu.

Dan shekaru 27 dai haihuwa, West Ham ta saye shi a bara akan pan miliyan shida daga Livorno.

Adreshin yanar gizon West Ham ya ce "Mun sayarda shi don mu siyo wasu 'yan kwallon".

A halin yanzu dai an doke West Ham a duka wasanninta biyu na gasar premier a kakar wasa ta bana, kuma ana saran za ta sayi dan kwallon kungiyar Lorient mai suna Kevin Gameiro.