Dan kwallon Masar Mido ya kara komawa Ajax

Mido
Image caption Mido ya fara taka leda a Zamalek

Dan kwallon Masar Mido ya kara komawa kungiyar Ajax ta Holland a kwangilar shekara guda daga kungiyar Middlesbrough.

Dan shekaru 27 da haihuwa, Mido ya kara hadewa da kungiyar ta Amsterdam wacce ya ciwa kwallaye 21 cikin wasanni 48 daga shekara ta 2001 zuwa 2003 kafin ya tafi Marseille akan pan miliyan takwas da dubu dari hudu.

Kocin Ajax Martin Jol yace"Muna bukatar karin dan kwallon gaba shi yasa muka sayo shi".

Mido ya taka leda a kungiyoyi goma daban daban tun daga kasarshi a Zamalek har zuwa Celta Vigo da Roma da kuma West Ham.