Ma'aikatan kididdiga sun shiga yajin aiki a Nijar

Nijar na kokarin rajistan masu zabe
Image caption Nijar na kokarin rajistan masu zabe

A jamhuriyar Nijar ma'aikatan kididdiga masu zabe sun shiga wani yajin aiki domin neman kwamitin rejistan masu zabe da suke yiwa aiki ya biya su albashinsu na kwanaki 20 da suka yi suna aiki akasin kwanaki 15 da ya kamata a biya su.

Haka zalika suna bukatar ma a kara musu albashin daga jika 3 na CFA zuwa jika 5 kowace rana ,sannan a kara kyautata musu yanayin aikinsu.

Kwamitin rejistan masu zaben na ganin neman karin zai yi wuya don kuwa bai da halin yin hakan.

Wannan yajin aikin dai ka iya mayar da hannun agogo baya ga tafiyar aikin.

Aranar 19 ga watan satumba ne kwamitin ya yi alkawarin mika ma hukumar zabe CENI kammalallen aikinsa na jerin sunayen masu zabe wanda da shi ne za a yi wa kowa katin zabe.