Geremi ya koma kungiyar Larissa a Girka

Geremi Njitab
Image caption Geremi Njitab

Dan wasan Kamaru Geremi Njitap ya sa hannu a kwantaragin shekaru biyu domin takawa Kungiyar Larissa ta kasar Girka leda.

Dan wasan wanda ya bugawa kungiyar Newcastle United da Real Madrid da kuma Chelsea a baya, ya koma Girka ne daga kungiyar Ankaragucu a Turkiyya.

A yanzu haka dai Geremi ya hade da dan wasan Gabon dake takawa kungiyar Hull City a da leda Daniel Cousin a kungiyar ta Larissa.

Larissa ce ta kare a matsayin ta takwas a kakar wasan bara a gasar Girka.